Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Sudan Su Na Nuna Alamu Kishiyoyin Juna A Kan ko Kasar Ta Yarda Da Shirin Girka Sojojin Kiyaye Zaman Lafiya Na MDD


Jami'an Sudan su na nuna alamu kishiyoyin juna a kan ko gwamnati ta amince da kafa rundunar kiyaye zaman lafiya ta hadin guiwa a tsakanin Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Kasashen Afirka a yankin Darfur mai fama da fitina.

A lokacin da yake magana yau Jumma'a a gidan rediyon kasar, ministan harkokin wajen Sudan, Lam Akol, ya ce bai kamata a yi maganar kafa rundunar hadin guiwa ba. Ya ce kasarsa ta amince da rundunar Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka ce, wadda zata samu taimakon MDD.

Amma kuma a cikin kalamun da yayi wa 'yan jarida, wani babban mashawarcin shugaba Omar al-Bashir na Sudan, Majzoub al-Khalifa, bai fito a fili ya musanta ra'ayin kafa rundunar hadin guiwa ba.

Jiya alhamis, babban sakataren MDD, Kofi Annan, ya ce Sudan ta yarda bisa manufa da batun kyale rundunar hadin guiwa ta MDD da Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka a Darfur. Mr. Annan ya bayyana wannan a bayan da aka yini ana gudanar da tarurrukan manyan jami'an diflomasiyya a Ethiopia. Babban sakataren ya ce wannan runduna da ake son kafawa a Darfur zata iya kunsar sojoji dubu 17 da 'yan sanda dubu uku.

XS
SM
MD
LG