Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministan harkokin wajen Syria yayi kira da'a fara shirin kwashe sojojin kasashen Waje daga Iraq


Ministan harkokin wajen kasar Syria wanda ya kai wata ziyarar kullan dangon Diplomasiyya a birnin Bagadaza, ya yi alkawarin baiwa gwamnatin iraq goyon bayan kana ya yi kira da’a shirya lokacin da sojojin kasashen waje za su fice daga kasar Iraq. Bayan da ya kare wata ganawa da ministan harkokin wajen kasar Iraq Hoshiyar zebari jiya lahadi, minister Walid al-Moualem na Syria ya ce kasarsa ta la’anci abinda ya kira ta’addanci a Iraq kana ya yi kira da’a janye sojojin amirka da domin a sami sukunin kawo karshen yakin jinsin addini a kasar.

Wannan ziyara tasa itace ta farko da wani babban jami’in gwamnatin kasar Syria ya kai kasar tun bayan da aka hambare gwamnatin Saddam Husaini a shekara ta 2003 kuma yayita a daidai lokacinda ake Karin kira akan Amirka data nemi hadin kan kasashen Syria da Iran wajen warware rikicin kasar Iraq. A lokacin ziyarar tasa, an sami karuwar tashin hankali a sassan kasar Iraq.

Jami’an tsaron kasar Iraq sunce ‘yan gwagwarmaya sun kashe akallan mutane 50 kuma sun kama mataimakin ministan kiwon lafiyar kasar Ammar Al-Saffar wani dan Shi’a.

XS
SM
MD
LG