Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rwanda Ta Tsinke Huldar Jakadanci Da Faransa


Rwanda ta tsinke huldar jakadanci da kasar Faransa, a bayan da wani alkali na Faransa ya bayar da takardun tuhuma tare da iznin kama wasu mutane dangane da kashe-kashen kare-dangi da aka yi cikin 1994 a Rwanda.

Ministan harkokin wajen Rwanda, Charles Murigande, ya fadawa Muryar Amurka yau Jumma'a cewa, "Faransa ta kuduri aniyar ganin bayan gwamnatinmu." Ya ce gwamnati ta umurci jakadan Faransa da ya bar kasar cikin sa'o'i 24.

Tun da fari, Rwanda ta bukaci jakadanta dake Faransa da ya koma gida. Ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta ce ta ji takaicin wannan shawara da Rwanda ta yanke.

Wani alkalin Faransa yana kokarin yin shari'ar wasu mukarraban shugaba Paul Kagame na Rwanda su tara bisa zargin cewa su na da hannu a harbo jirgin saman shugaban Rwanda na lokacin, Juvenal Habyarimana, da shugaban Burundi, Cyprien Ntaryamira, ranar 6 ga watan Afrilun 194.

Harbo jirgin dake dauke da shugaban Rwanda dan kabilar Hutu na farko da aka taba zaba, ya harzuka 'yan Hutu masu tsattsauran ra'ayi, ya kuma janyo kashe-kashen da aka shafe kwanaki dari daya ana yi har aka kashe mutane kimanin dubu dari takwas, 'yan kabilar Tutsi marasa rinjaye da 'yan kabilar Hutu masu sassaucin ra'ayi.

XS
SM
MD
LG