Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kona Masallatan 'Yan Mazhabin Sunni Da Dama Yau Jumma'a A Bagadaza


Wasu mutanen da ake kyautata zaton sojojin sa kai na 'yan mazhabin Shi'a ne sun kai farmaki kan masallatan 'yan mazhabin Sunni yau Jumma'a a birnin Bagadaza, a wani matakin da ake dauka a matsayin ramuwar gayyar hare-haren bam da suka kashe mutane fiye da maitan kwana guda kafin nan.

Shaidu a Bagadaza sun ce sojojin sa kai sun harba rokoki tare da bude wuta da bindigogi masu jigida, sannan suka cunna wuta a wasu masallatai guda hudu a wani bangare na farmaki kan 'yan mazhabin Sunni a unguwar Hurriyah ta birnin.

Rahotannin farko sun ce an kashe mutane akalla 24.

A halin da ake ciki, sojojin sa kai sun gwabza da sojojin Amurka yau jumma'a a Unguwar Sadr ta Bagadaza, inda aka kai munanan hare-haren bam na jiya alhamis. A nan Washington, gwamnatin shugaba Bush ta bayyana hare-haren bam na jiya alhamis a zaman aiki maras kan gado. Harin shi ne mafi muni da aka taba kaiwa tun lokacin da aka kaddamar da yaki kan Iraqi a 2003.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Annan, yayi tur da hare-haren, ya kuma yi kira ga dukkan 'yan Iraqi da su kai zuciya nesa domin hana wannan lamari kara yin muni.

'Yan'uwa masu jimami su na binne gawarwakin mutanen da aka kashe a hare-haren bam na alhamis. Firayim minista Nouri al-Maliki ya umurci 'yan sanda da su yi gadin jerin masu jana'iza dake yin tattaki daga Bagadaza zuwa birnin Najaf mai tsarki ga 'yan mazhabin Shi'a.

XS
SM
MD
LG