Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Rikon Kwarya Ta Somaliya Ta Yi Marhabin Da Iznin Tura Sojojin Kiyaye Zaman Lafiya Da Majalisar Dinkin Duniya Ta Bayar


Gwamnatin rikon kwarya ta Somaliya ta yi marhabin da matakin da Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ta dauka na amincewa da tura sojojin kiyaye zaman lafiya na Afirka zuwa kasar mai fama da fitina.

Firayim minista Ali Mohammed Gedi ya fada yau alhamis cewa ana bukatar ’yan kiyaye zaman lafiyar domin hana mutanen da ya kira ’yan ta’adda gurgunta Somaliya da yankin kuryar arewa maso gabashin Afirka.

Amma kuma shugabannin kungiyar ’yan kishin Islama mai karfi da tasiri a Somaliya sun ce ba za su taba amincewa da sojojin kasashen waje ba, kuma za su yake su idan suka sa kafa a kasar.

Jiya laraba, Kwamitin Sulhun MDD ya bayar da iznin girka sojojin kiyaye zaman lafiya domin kare gwamnatin rikon kwarya maras karfi a Somaliya. Har ila yau kudurin ya sassauto da takunkumin makamai da aka sanyawa Somaliya shekaru 14 da suka shige, domin ’yan kiyaye zaman lafiyar su samu zarafin horaswa tare da tallafawa sojojin gwamnati.

Har ila yau kudurin yayi kira ga masu kishin addinin da su dakatar da ci gaba da kai farmakin soja su koma kan teburin shawarwarin zaman lafiya da gwamnati. Masu kishin addinin Islama sun kwace akasarin yankunan kudanci da tsakiyar Somaliya a wannan shekara.

XS
SM
MD
LG