Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Falasdinawa Wadanda Ba Su Ga-Maciji Da Juna Sun Gwabza A Gaza Da Yammacin Kogin Jordan


Falasdinawa 'yan bindiga wadanda ba su ga maciji da juna sun gwabza a Gaza da kuma garin Ramallah a yankin yammacin kogin Jordan, kwana guda a bayan wani mummunan harin da aka kai kan ayarin motocin firayim ministan Falasdinu.

An kwana biyar ke nan a jere ana kai ruwa rana a tsakanin kungiyar Hamas mai mulkin yankunan Falasdinawa da abokiyar adawarta Fatah ta shugaba Mahmoud Abbas. Mutane akalla 32 sun ji rauni a fadan yau Jumma'a.

Wannan fadan, na yau Jumma'a, ya biyo bayan zargin da Hamas ta yi cewar 'yan bindiga na kungiyar Fatah sun yi kokarin hallaka firayim minista Isma'il Haniyeh.

An kashe daya daga cikin dogarawan firayim ministan a harbin bindiga jiya alhamis a kusa da bakin iyakar Gaza da Misra. Kungiyar Fatah ta musanta cewa da hannunta a wannan farmakin. Shugaba Mahmoud Abbas ya bayyana takaicin al'amarin.

Duk da wannan tashin hankalin, dubun dubatan 'yan kungiyar Hamas sun yi gangami yau Jumma'a a birnin Gaza domin murnar cikar shekaru 19 da kafa kungiyar.

A cikin wani jawabin da yayi da lafazi mai zafin gaske, firayim minista Haniyeh ya ce ba wai 'ya'yan Hamas su kan shiga kungiyar domin su zamo ministoci ba ne, sai domin su yi shahada.

XS
SM
MD
LG