Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Ta Kara Tsawon Wa'adin Aikin Sojojin Kiyaye Zaman Lafiya A Ivory Coast


A wani matakin bai-daya, Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya yarda da kara wa'adin aikin sojojin kiyaye zaman lafiya na majalisar da na Faransa dake kasar Ivory Coast har zuwa ranar 10 ga watan Janairu.

Da, a yau jumma'a ne wa'adin aikin sojojin kiyaye zaman lafiyar MDD su kusan dubu takwas, da na Faransa su dubu biyu zai cika.

Har ila yau, Kwamitin Sulhun ya amince da kara wa'adin watanni shida na ci gaba da aikin wasu kwararru dake sanya idanu a kan takunkumin da aka sanyawa wasu mutane a kasar Ivory Coast. A cikin watan Fabarairu jami'an MDD suka dauki matakan haramta yin tafiye-tafiye tare da garkame asusun ajiyar bankuna na wasu mutanen da aka yi imanin su na kawo cikas ga kokarin wanzar da zaman lafiya a Ivory Coast.

Majalisar tana sanya idanu a kan gwamnatin rikon-kwarya da shirin wanzar da zaman lafiyar da ake kokarin shimfidawa da nufin sake hada kan kasar, wadda tun yakin basasar 2002 take rarrabe.

XS
SM
MD
LG