Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Palasdinawa su tsagaita bude wuta amma sai..


Bangarorin palasdinawa dake gaba da juna sun tafka kazamin fada yau Talata a zirin gaza duk da cewa har yanzu shirin tsagaita bude wuta na kwanaki biyu tsakaninsu yana aiki. Jami’an asibiti suyce a kallan mutane 5 sun mutu daga cikh har da wani jami’in ‘yan sandan Hamas biyu. da kuma jami’an tsaron jam’iyar Fatah su biyu. Shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas na jam‘iyar Fatah ya kirayi duk bangarorin akan su daina budewa juna wuta.

Firayi-ministan Palasdinu Isma’il haniyeh shima ya soki Amirka da laifin jagorancin wani kokari na ture gwamnatin Palasdinawa da Hamas kewa Jagoranci. A daidai lokacin da fadar taka bazuwa zuwa sassan yankin, Sarki Abdullah na Jordan ya ce ashirye yake da niyar jagorancin zaman tattaunawa tsakanin bangarorin dake gaba da juna a yankin. Sarkin ya musu wannan tayin yau Talata a birnin Amman lokacin da yake tare da firayi-ministan Isra’ila Ehud Olmert.

XS
SM
MD
LG