Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Likitocin dabbobi a Najeriya sun koka game da illar murrar Tsuntsaye


Kungiyar Likitocin Dabbobi ta Najeriya ta ce annobar cutar murrar Tsuntsaye ta yadu zuwa sassan kasar masu yawa fiye da yadda aka zata ada. Tace nau'in cutar mai H5N1 har yanzu yana kasancewa babbar matsala a kasar kuma tayi Sunyi gargadin cewa wannan cuta na iya kunno wata annobar da ta fi abind aka sani abaya a kasar.

Mai Magana da yawun kungiyar likitocin Dabbobi ta Najeriya Bala Mohammed an sami Karin jihohin kasar da suka bada rahoton bullar wannan cuta a cikin ‘yan makonni da suka wuce. Ya ci gaba da cewa abinda muke cewa sake farfadowar gyauron cutarne yanzu yana bada tsoro. Abinda ya farad daga jihohi 10 yanzu yakai kusan duk johohin sun sami bullar wannan cuta. Wannan wani gagarimin kalu baleen agare mu a Najeriya kuma yana bukatar a sake duba duk matakan da aka dauka a da wajen yaki da cutar ayanzu. A cikin wata guda daya shige, Dokta Bala Mohammed ya ce jihon Delta da Akwa Ibom da Rivers da Cross Rivers, da kuma yankuna da dama a Lagos aka sami bullar wannan cutar.

Yanzu dai likitocin dabbobi a kasashen duniya suna jin Najeriya da wasu kasashen Afirka biyu ne suka kasa shan karfin wannan annobar cutar ta Tsuntsaye.

XS
SM
MD
LG