Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kama mutane hudu da ake tuhuma shugabannin kungiyoyin ta’adda ne


Rundunar Sojin Amurka a Iraqi, tace dakarun Iraqi na musamman sun kama mutane hudu da ake tuhuma shugabannin kungiyoyin ta’adda ne da suka kware wajen sata da kuma kisan farar hula a Iraqin. Sanarwar soja da aka bayar a yau juma’a tace dakarun na Iraqi, sun kama mutanen ne ranar laraba a unguwar Sadr inda akasari mazaunan ta yan mashabr Shi’ia ne a Bagadaza.Sanarwar tace kwararru daga sojojin kawance sun dafawa sjojin Iraqin baya a lokacin wannan farmaki.A awata sanarwa ta daban,rundunar tace a sun ceto mutane biyu da yan gwagwar maya suke garkuwa dasu,lokacin wani somamen da suka kai a gabashin Bagadaza. Sanarwar ta kuma ce sojojin sun kwace makamai iri daban daban da dama.
XS
SM
MD
LG