Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabbin Shugabannin Majalisun Dokokin Amurka 'Yan Democrat Sun Bukaci Shugaba Bush Da Kada Ya Tura Karin Sojoji Zuwa Iraqi


Shugabannin majalisun dattijai da wakilai na tarayya ’yan jam’iyyar Democrat sun bukaci shugaba Bush da yayi watsi da duk wani shirin kara yawan sojojin Amurka a Iraqi, su na masu fadin cewa dada yawansu zai kara iza wutar yakin da ake yi a can.

A cikin wata budaddiyar wasikar da suka aikewa Mr. Bush, sabuwar kakakin majalisar wakilai, Nancy Pelosi, da shugaban masu rinjaye a majalisar dattijai, Harry Reid, sun ce kara yawan sojojin zai jefa karin Amurkawa cikin hatsari ne kawai tare da girka sojojin Amurka fiye da yadda ya kamata ba tare da wata riba ba.

A mako mai zuwa shugaba Bush yake shirin bayyana sabuwar manufa kan kasar Iraqi, manufar da ya ce zata taimakawa ’yan Iraqi wajen cimma gurinsu na mulkin kansu da kare kawunansu. Kafofin labarai sun bayar da rahotannin cewa sabuwar dabarar shugaban zata iya hadawa da kara girka dubban sojojin Amurka na wani dan lokaci a Iraqi.

Har ila yau shugaba Bush yana shirin nada sabbin kwamandojin sojan Amurka a Iraqi da yankin Gabas ta Tsakiya.

XS
SM
MD
LG