Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sako daga ma'aikatar Rawarwa da kasashe ta USAID


Ga sakonnin riga kafin kamuwa da cutar murrar tsuntsaye Wanda ke iya yaduwa daga mutun zuwa Mutun daga USAID

Ga sakonnin riga kafin kamuwa da cutar murrar tsuntsaye Wanda ke iya yaduwa daga mutun zuwa Mutun daga USAID Ko da yake ba safai ake samun yaduwar wannan cuta daga mutun zuwa mutum ba, to To amma kwai lokuta da mutane suka kamu da kwayar wannan cuta nau’in H5N1, wa wajen cudanya tsuntsaye da suka kamu da kwayar cutar. Duk da haka wannan kada ya kawo rudewar hankali. Saboda wadannan lokuta da aka sami tsauyayin kamuwa da cutar yakamata a lura da wadansu matakai na kiyaye yadon cutar tsakamin mutane.

1· A wanke hannu da sabulu da ruwa ko maganin kwayayoyin cuta.

2· A rufe baki da mayani a lokacin da ake tari ko hatishawa.

3· Idan zai samu a zauna a gida kadda aje makaranta ko wajen aiki idan ana da alamun cutar ko ana ji a jiki. Halamar cutar mashasshara ta hada da murra mai tsanani.

Afahinci alamun cutar mashasharar tsuntsaye a jikin wanda ya kamu da ita kuma, kasan matakan da zaka dauka idan kana ji ka kamu da wannan cuta Mashasshar.

1· Ka yi maza ka kai rahoton alamun mashashsharan tsuntsaye a jikin mutun, idan kana jin zazzabi, tari jiri, tari da ciwo a jijiyoyinka. Ko kana jin ciwon ido kasala, ko kaikaci cikin makosarka, ko kana numfashi dakyar ko kuma duk wani irin rashin lafiya da baka taba jin irinsa ba a jikinka.

2· Idan kuma kana jin wani yanada cutar murrar tsuntsaye, kayi maza ka kaishi wajen likitoci su duba shi.

3· Kana iya zuwa ofishin kiwon lafiya na yankin da kake ko garin da kake cikinsa.

Ga kuma hanyar rigakafin kamuwar cutar tsakamin tsuntsaye

Akwai wata sabuwar cutar tsuntsaye da take saurin kisar kaji da sauran tsuntsaye. Ana kiranta Mashassharar Tsuntsaye, ko kum aH5N1 a nau’in cutar murrar tsuntsaye. Tana yaduwa tsakanin tsuntsaye ko kaji da ake ciwonsu a waje daya. Kaji ko sauran tsuntsaye na iya kamuwa da shi ta wajen kashi da suke yawo suna bazawa, ko cikin ruwan da masu cutar suka sha suka bari, idan masu lafiya sun sha suna iya kamuwa. Mutane da tsuntsaye na iya kamuwa da wannan cuta. Don haka a kara kiyayewa.

XS
SM
MD
LG