Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Tsaron Kasar Guinea Su Na Ci Gaba Da Yin Arangama Da Masu Zanga-Zanga


Dakarun tsaro na kasar Guinea su na ci gaba da yin arangama da masu zanga-zanga dake fusace, a yayin da yajin aiki na gidan-kowa-da-shi ya shiga rana ta tara da farawa.

Rahotanni daga ciki da wajen Conakry, babban birnin kasar alhamis din nan, sun ce masu zanga-zanga sun gudanar da tarurruka da gangami, a wasu wuraren kuma sun gwabza da 'yan sanda. An samu rahotannin zanga-zanga a wasu biranen larduna da dama.

A halin da ake ciki, shugabannin kwadago sun ce shugaba Lansana Conte yayi musu barazana, ya kuma zazzage su lokacin wata ganawar da suka yi jiya laraba. Suka ce taron ya watse a lokacin da shugaban, mai fama da tsufa da rashin lafiya, ya nuna alamun gajiya. Suka ce ko musafaha ya ki yarda yayi da su.

Wannan yajin aiki da ake yi ya kai ga rufe ramin hakar karfen goran ruwa mai suna CBG dake samar ad dimbin kudi, yayin da kuma aka rufe akasarin kantuna da kamfanoni har ma da ofisoshin gwamnati.

Shugabannin kwadago da suka shirya yajin aikin sun yi kira ga shugaba Conte da ya sauka a kafa sabuwar gwamnati karkashin jagorancin firayim minista farar hula.

XS
SM
MD
LG