Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mataimakin shugaban Najeriya Alh. Atiku Abubkar ya gabatar da shirin yakin Neman zabe


A wannanTalalatar, Mataimakin shugaban Nigeria Alhj. Atiku Abubakar ya kaddamar da shirinsa na yakin neman zaben zama shugaban Nigeria a babban zabe da za’ayi a kasar a watan Afirillu. Atiku Abubakar yana takara a karkashin inuwar jam’iyar AC bayan da jam’iyarsa ta PDP dake rike da ragamar mulkin kasar ta koreshi daga jam’iyar a watan jiya bisa zarginsa da ta yi da laifin cin hanci. Duk da haka ya musanta wannan zargin sannan yace an dai koreshi ne saboda siyasa.

Kakakin Atiku Abubakar, Shehu Garba yace jamiyar AC zata bude ofishin yakin neman zabenta kuma zata gabatar da ayarin ‘yan yakin neman Zaben Atiku abubakar ayau Talatar kuma zata yi wagani gagarimin gangamin yakin neman zabe a garin Kano wani lokaci a wannan makon. Shugaban Nigeria Chief Obasanjo ya bukaci Atiku Abubakar da yayi murabus daga mukaminsa saboda canza sheka da yayi ya shiga wata jam’iyar AC.

A bara ne dangantaka tsakanin shugabanin biyu na Nigeria ta yi tsamari bayan da Atiku Abubakar ya turjewa wani kokari da Obasanjo ya yi na gyara tsarin mulki da zai bashi damar rike karagar mulkin kasar a karo na uku.

XS
SM
MD
LG