Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Kasar Philippines Da AkeGarkuwa Da Su A Nijeriya Su Na Cikin Koshin Lafiya


Jakadan Philippines a Nijeriya ya ce ’yan kasarsa su 24 da aka sace watan jiya a Nijeriya suna nan cikin koshin lafiya.

Jakada Masaranga Umpa ya ce ya samu wannan labari jiya laraba daga bakin wani jami’in tattaunawa na gwamnatin Jihar Delta, Ovie Omo-Agege. Umpa ya ce jami’in ya fada masa cewa shi da kansa ya ga mutanen da ake yin garkuwa da su a ranar 30 ga wata, watau shekaranjiya, kuma lafiyarsu kalau. Ya ce jami’in shawarwarin ya fada masa cewar yana fuskantar wahala wajen tattaunawa da wadanda suka yi garkuwa da ’yan Philippines din, amma kuma yayi imanin za a iya warware wannan matsala.

An sace ma’aikatan jirgin ruwan ’yan Philippines ranar 20 ga watan Janairu daga wani jirgin daukar kaya a birnin Warri na kudu maso yammacin kasar.

Kungiyoyin ’yan daba su na kai hare-hare tare da sace mutane a yankin na Niger Delta mai arzikin mai. ’Yan ta kifen suna neman gwamnati ta kara sakarwa da mutanen yankin bakin aljihun arzikin man da ake tona cikin yankin.

XS
SM
MD
LG