Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Najeriya an sami bullar cutar murrar tsuntsaye a jihohi19 da Abuja


Mahukuntan Nigeria sunce an sami labarin bullar cutar murrar tsuntsaye a jihohi 19, daga ciki harda birnin Abuja babban birnin kasar. kuma wannan matsalar tana janyo fargaban yadon cutar zuwa wasu sassan kasar. Wani saboron rahoto da gwamnatin kasar ta bayar na baya bayan nan yace kwayoyin cutar nau’in H5N1 suna cigaba da yaduwa, zuwa gonakin kiwon kajin kasar.

Kusan shekara guda da ta shige ne aka bada labarin dan adam ya kamu da cutar bayan da Nigeria ta bada labarin nata cutar wanda ta kama dan adam na farko. Tun daga wancan lokacin wannan kasa ta yammacin Afirka ta cigaba da kokarin tinkarar yadon kwayoyin wannan mugguwar cutar.

Kwararrun likitocin da suka san kwayoyin cutar mashassharan tsuntsaye suna zullumin cewa Nigeria na iya kasancewa mazaunin wannan cuta na dindindin. Wani likitan dabbobi Dokta Garba sha’rubutu, kuma shugaban kungiyar likitocin dabbobi ta Nigeria, yace bisa tarihi a Nigeria idan cuta irin wannan ta bulla ba kowa yake taimakawa a wajen yaki da ita.

Yace yakamata gwamnatita sa jami’an, da kungiyar dibobi su su hana safaran kaji da wasu tsuntsaye ta motoci daga sassa daban dabam na kasar. Haka kuma a umurci sarakunan gargajiya suma su taimaka wajen bada labarin cutar idan sunji ta kashe ko tsuntsaye na garuruwansu.

XS
SM
MD
LG