Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Wakilan Amurka Ta Zartas Da Kudurin Rashin Yarda Da Tura Karin Sojoji Zuwa Iraqi


Majalisar Wakilan Tarayya ta Amurka ta zartas da kudurin nuna rashin yarda da matakin da shugaba Bush ya dauka na tura karin sojoji zuwa Iraqi.

'Yan majalisa 246 suka amince da kudurin, yayin da wasu 182 suka jefa kuri'ar kin amincewa. 'Yan jam'iyyar Republican da dama sun bi sahun kusan dukkan 'yan Democrat wajen amincewa da kudurin wanda ba tilas a yi aiki da shi ba, wanda ya soki manufofin shugaba Bush a Iraqi. Majalisar tana da wakilai 435.

Kudurin ya bayyana ci gaba da goyon baya ga sojojin Amurka dake Iraqi, yayin da ya bayyana adawa da tura karin sojoji fiye da dubu 20 zuwa can.

Wannan kuri'a ita ta kawo karshen muhawara mai zafi ta kwanaki hudu da aka yi a majalisar da 'yan Democrat asuke jagorancinta.

Wannan shine karon farko da majalisar dokokin Amurka ta jefa kuri'ar nuna adawa da manufar shugaba Bush game da yakin Iraqi tun lokacin da aka mamaye kasar a watan Maris na 2003. Zartas da wannan kuduri yana iya share fagen zartas da kudurori na doka a kan wannan rikicin da ya zuwa yanzu ya kashe sojojin Amurka fiye ad dubu uku da dari daya.

Kakakin majalisar wakilan, Nancy Pelosi 'yar Jihar California ta fadawa majalisa cewa su na aza harsashin sabuwar alkibla ce a Iraqi wadda zata maido ad sojojin Amurka gida kuma ba da dadewa ba. ta ce shirin shugaban tamkar nanata kura-kuran da aka yi a can baya ne, kuma zai yi wuya su cimma kai ga nasara.

'Yan Republican da dama a majalisar sun yi kashedi game da mummunan sakamakon da tsaron Amurka zai fuskanta idan har ta kasa samun nasara a Iraqi.

XS
SM
MD
LG