Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Likitoci a Rasha suna gwajin wasu matattun kaji


Likitocin dabbobi suna gwajin wasu tsuntsaye da aka sami gawarwakinsu a kusa da birnin Moscow bayan da aka tabbatar da cewa akwai nau’in H5N1 ta cutar murran tsuntsaye a jikin wadansu matattun tsuntsaye da aka samu a lardunan kasar biyar dake kuma da babban birnin kasar a makon jiya.

Jami’an kiwon lafiyar dabbobin sun fada ranar Talata cewa suna jin cewa mashsharan tsuntsaye ne ta kashe kaji wajen 75 a wata gona dake yankin gabashin birnin Moscow.

A garinRamenskoye ntun ranar Asabar da ta shige. Likitoci suna ci gaba da auna samfurin da suka dauka a jikin naman kajin domin tantancewa ko kajin sun mutune daga murrar tsuntsaye, wacce ta kashe mutne wajen 160 aduk fadin duniya a shekara ta dubu biyu da uku. Mahukuntan kasar sunce tsuntsayen gida kusan, dari 200 ne suka mutu a kusa da birnin Moscow acikin kwanaki 10 da suka wuce.

Jami’an kiwon lafiya da kuma likitocin dabbobi sun hakkake cewa kebe tsuntsaye masu cutar da kuma tsabtace muhallinsu ya taiamaka wajen kare yadon cutar. Lauyoyin kasar Rasha sun bada rahoton cewa ana binciken ganin ko an keta dokokirin kiwon tsuntsaye ne ya janyo sabon bullar cutar.

XS
SM
MD
LG