Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Tana Kokarin Magance Sabbin dabarun 'Yan Gwagwarmaya A Iraqi


Mataimakin babban kwamandan sojojin Amurka a Iraqi ya ce dakarunsa suna kokarin shawo kan sabbin dabaru biyu da ’yan gwagwarmaya suka bullo da su, watau kaifin harbo jiragen helkwafta masu saukar ungulu da kuma wani sabon bam da ake surka shi da iskar gas mai guba ta Chlorine.

Da yake magana da 'yan jarida a hedkwatar ma'aikatar tsaron Amurka ta tauraron dan Adam daga Bagadaza, Leftana-janar Ray Odierno ya ce a cikin wata gudan da ya shige, an harbo jiragen saman helkwafta guda 8 na kasashen kawance, kuma dakarunsa sun fara samun bayanai a kan hanyoyi da kuma dalilan da hakan ke faruwa. janar Odierno ya kara da cewa, "...muna ganin wasu dabaru da take-taken da ba na son yin sharhi a kansu yanzu. A saboda haka, muna sane da abubuwan da suke yi muna kuma kokarin fahimtar wadannan abubuwa, da gano su ta yadda zamu iya kare jiragenmu, tare da farauto gungun masu aikata wannan."

Janar Odierno ya ce a makon da ya shige, sojojin taron dangi sun tsare wani mutumin da suka yi imanin yana daya daga cikin gungu-gungun, kuma a cikin ’yan kwanakin da suka shige sun kama wasu karin mutanen a sumamen da suka yi ta kaiwa cikin dare. Janar din yayi imani wadannan gungu-gungu su na da alaka da kungiyar ta’addanci ta al-Qa’ida.

Janar Odierno ya ce kare jiragen helkwafta yana da matukar muhimmanci a saboda hukumomi sun dogara kansu sosai domin sufuri. Ya ce amfani da jiragen helkwafta zai ninku sau biyu a wannan shekara idan an kwatanta da shekaru biyun da suka shige.

Haka kuma janar Odierno yayi magana a kan amfani da iskar Chlorine mai guba da ’yan gwagwarmaya suka yi sau uku cikin ’yan kwanakin nan. Ya ce sojojinsa sun gano irin wannan gas a wata masana’antar kera bama bamai ta ’yan gwagwarmaya da suka kai ma sumame ranar talata a kusa da Fallujah. Sun kuma gano nakiyoyi da kunamu da wasu motoci hudu ana harhada musu bama-bamai masu karfi.

A cewar janar Odierno, "Abinda suke kokarin yi shi ne sauya dabarunsu ta hanyoyin da zasu iya ci gaba da haddasa rashin kwanciyar hankali. Abinda suke yi ke nan, musamman ma da iskar gas din Chlorine da suke hadawa da nakiyoyi. Wannan wata hanya ce da suke kokarin runguma domin haddasa fitina a kasar nan."

Janar din ya ce bai ga wata alamar dake nuna cewa akwai hannun Iran a samar da wannan iskar gas mai guba ta Chlorine ba. Kwanaki goma da suka shige, wasu jami’an sojan Amurka dake Bagadaza, sun fada bisa sharadin cewa ba za a bayyana sunayensu ba, cewar jami’an Iran suna samar da fasahar kera bama bamai da kayan hada su ga ’yan gwagwarmayar Iraqi.

A jiya alhamis, janar Odierno ya bi sahun wasu manyan jami’an dake cewa ba su da tabbas ko akwai hannun manyan jami’an gwamnatin Iran kamar yadda jami’ai na farko suka yi zargi.

XS
SM
MD
LG