Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hannun jari ya dan tashi a kasuwar hada hadar kudi


Yau Laraba Masu zuba jari a Amurka da nahiyar Asiya suka kara karyar da hannayen jarinsu a kasuwannin zuba jari, bayan da jarin kasar sin yayi zubar kago, kuma yaci gaba da shafar kasuwannin duniya. Kasuwannin Nikkei na Japan, da Hang Seng na Hong Kong duk sun sami karayar kashi uku-uku bisa dari, ta kasar Philippines kuma ta zube da kashi takwas bisa dari. Kasuwannin Jarin Shangai sun fara farfadowa, da misalin kashi hudu bisa dari a yau, bayan karayar kashi tara bisa dari a jiya Talata.

A safiyar yau ma yawancin kasuwannin jarin Turai sun da tabu da kashi daya da rabi bisa dari ko ma fiye da haka. Masu fashin bakin al’amuran tattalin arzikin kasashen duniya, sunce karayar tattalin arzikin kasuwannin duniyan, zata iya kasancewa sakamakon karon battar da ake shirin yi tsakanin tattalin arzikin Kasar Amurka da na Sin.

A jiya Talata jari kasuwar Wall Street yayi faduwar da bai taba yi ba tun daga 11 ga watan Stumban 2001, wato lokacin da aka kaiwa cibiyar kasuwanci ta World Trade Centre hari. Kasuwannin Kasashen Latin da na Turai suma sun tabu kwarai daga wannan matsalar ta karyewar kasuwannin zuba jari.

XS
SM
MD
LG