Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yar Aduwa Yana Nan Da Ransa


Dan takarar Shugaban Kasa a karkashin tutar Jam’iyyar PDP, Alhaji Umaru Musa ‘Yar Aduwa ya karyata labarai da ake bazawa cewa ya mutu. Yayi Wannan bayani ne a wata hira da Muryar Amurka, daga wani asibiti a kasar Jamus.

Gwamna Umaru Musa ‘Yar Aduwa, wanda a halin yanzu ake duba lafiyarsa a wani asibiti dake garin Wiesbaden na kasar Jamus, ya maida martani tare da raha, ga labaran mutuwarsa da akai ta bazawa, inda yace wannan alama ce dake nuna cewa ta zai yi tsawon rai. Yace babu gaskiya a labaran rasuwarsa, duk da cewa baya zargin kowa da yada wadannan labarai. Ya godewa ‘yan Najeriya saboda damuwar da suka nuna a kan halin da yake ciki, ya kuma bukacesu suci gaba da addu’a.

Alhaji Umar Musa ‘Yar Aduwa ya nusar da jama’a cewa da rai da mulki duk na Allahn ne, kuma yana bayarwa ga wanda yaso. Ya bayar da tabbacin cewa da zarar ya kammala abubuwan da suke gabansa zai dawo gida yaci gaba da yakin neman zabe. Da safiyar Laraba mutanen najeriya suka tashi da jita jitar rasuwar dan takarar. Jami’an Yakin neman zabensa sunce har yanzu basu kaiga samo inda wannan jita jita ta samo asali ba.

XS
SM
MD
LG