Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

PM Isra'ila yace aguje zai je taron kungiyar Larabawa idan sun gayyace shi.


Firayi ministan Isra’ila Ehud Olmert yace ya zai bata lokaci ba wajen halartan taron kungiyar kasashen larabawa da za’ayi idan sun gayyaceshi. Litinin din nan ne Mr Olmert ya bayyana hakan inda ya ce zai dubu takardan gayyata da zasu aike masa da idon harama.

Ya fadi hakan ne a wajen wani taro a birnin Kudus wajen ganawarsa da kakakin Majalisar Dinkin duniya Ban ki Moon. Mr. ban yace ya roki PM Isra’ilan daya sake nazari akan matakin da ta dauka na kin sabuwar gwamnatin Palasdinawa ta da ta kunshi jami’an kungiyar Hamas wacce take amincewa da kafuwar Isra’ila a matsayin kasar. Sakatariyar harkokin wajen Amirka Condeleezza Rice itama ta na ‘yankin gabas ta tsakiya domin tattaunawar zaman lafiya tsakanin palasdinawa da Isra’ila.

A yau Litinin ta gana da sarki Abdullah na Jordan da shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas kafin fara tattaunawa tsakaninta da jami’an Isra’ila da birnin Kudus. Rice tace tana son ta hanzarta shirya zaman tattaunawa tsakanin Isra’ila da palasdinawa. A gefe guda kuma a wani zantawa da tsakanin Mr Abbas da Mr Olmert jiya lahadi Sakatariyar ta rokesu akan su sake dago da shirin zaman lafaiya tsakaninsu kuma su yi kokarin kafa kasa mai zaman kanta ta palasdinawa.

XS
SM
MD
LG