Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu ’yan bindiga a yankin Darfur na yammacin Sudan sun kashe sojojin kiyaye zaman lafiya su biyar


Kungiyar kasashen AfriKa tace wasu ’yan bindiga a yankin Darfur na yammacin Sudan sun kashe sojojin kiyaye zaman lafiya na Kungiyar su biyar, Kisa mafi muni data auku tun lokacinda aka tura sojojin a shekara ta dubu biyu da hudu. Wani mai magana da yuwun kungiyar ƙasashen Afrika yace jiya lahadi da dare aka kai wannan hari a yayinda sojojin ke gadin kan iyakar kasar da Chadi. Ya fadawa Muryar Amirka cewa ba’ tsokane su suka kai wannan hari kuma ana binciken al’amarin.

Hudu daga cikin sojojin nan take suka mutu, na biyar kuma da sanyi safiyar yau litinin ya mutu a saboda raunin daya jiya. Maida wutar da sojojin suka yi ta kashe uku daga cikin ’yan bindigan da ba’a san ko su wanene ba. Wannan al’amari ya faru ne kwana ɗaya bayan da wasu mahara da ba’a san ko su wanene ba suka buɗe wuta akan jirgin sama mai saukar angulu na ƙungiyar ƙasashen Afrika dake wucewa ta sararin samaniyar Darfur.

Sojoji kiyaye zaman lafiya na ƙungiyar guda goma sha biyar ke nan aka kashe tun lokacinda suka isa Darfur a shekara ta dubu biyu da huɗu. Yanzu haka ƙungiyar tana da kimamin sojoji dubu bakwai data tura Darfur, to amma kuma Sudan taƙi a tura rundunar sojan kiyaye zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya masu yawa domin su taimakawa sojojin kiyaye zaman lafiya na ƙungiyar ƙasashen Afrika waɗanda ke fama da matsalar rashin na gwamnan masu gida rana, gashi kuma aiki yayi musu yawa.

XS
SM
MD
LG