Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar sojin Amirka a Iraq ta nuna damuwa


Rundunar sojin Amirka tace hankalinta na tashi game da irin harin bama bamai da ake kaiwa manyan jami’an kasar duk kuwa da ganin cewa sabbin matakan tsaro da aka dauka sun rage fadace fadacen jinsunan addinin kasar a Bagadaza.

Kakakin Rundunar sojin Amirka Manjo janar William Caldwell yace tashe tashen hankulan jinsunan addini da suka hada da kashe mutane da ta hanyar dabara duk sun takaita da kimanin kashi 26 daga cikin dari a babban birnin kasar a cikin watan jiya idan aka kwatanta da watan fabarairu.

Duk da haka janar Caldwell ya nuna damuwa game da hare haren bam na kwanan nan da suka kashe ‘yan kasar da dama suka suka jiwa da yawa ciwo. A Wani tashin hankali na yau Laraba wasu‘yan bindiga ne suka yiwa wata motar safa dake dauke da ma’aikatan wutan lantarki kwanton bauna a garin Kirkuk dake arewacin kasar suka kashe akallan mutane 6. ‘yan sandan Iraq sunce ‘yan bindigar sun sace wasu makiyaya 22 a kusa da birnin Karbala a kudu maso yammacin Bagadaza.

XS
SM
MD
LG