Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Lafiay ta duniya tayi kira da'a kara maida hankali


Hukumar Lafiya ta Duniya tana kira da’a kara bada hadin kai tsakanin kaashen duniya wajen yaki da safarar tsunyaye ta kan iyakar kasashe abinda ke barazana ga lafiyar jama’a. Wajen bukin ranar lafiya ta Duniya da aka yi a karshen mako ne hkumar ta bada wani rahoto dake gargadi gane da barazanar lafiya dake yawo tsakanin kasa da kasa.

Rahoton yace cututtuka kamar su Cutar kanjamau, da Zazzabin Ebola da kuma mashasharar SARS da suka bulla a kasashen Asiya da kuma cutar murrar Tsuntsaye dake kama bani Adama suna bulla a wurare da aba’a tsammani.

Hukumar Lafiya ta ce matsalar annoba iri iri da ake gani da gurbatar yayani da dottin masana’antu kle janyowa da kuma gurbata koguna da koramu da magunguanar ayyukan masana’antu keyi suna dada kara barazana ga rayuwar jama’a.

XS
SM
MD
LG