Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar sojin Amirka tace  mutane 8 aka kashe a Bagadaza


Wani mai magana da yawun rundunar sojin amirka a Iraq yace harin bam da aka kai yau cikin majalisar dokokin kasar a bagadaza, ya kashe mutane 8 sannan 20 kuma sunji rauni. Sojan Amirka janar Williams Cadwell, yace dan kunar bakin waken ya tada bam din ne wanda yayi jigida da shi.

CaldWell yace harin Bam din yayi kama da na kwanaki wanda wani dan Alka’ida yakai. Jami’an kasar Iraq sunce uku daga cikin mutanen da suka rasa ransu ‘yan majalisa ne. An kai harin ne dakin cin abinci na majalisar kuma an bayyana shi amatsayin barazana ga shirin tsaro a yankin nan na Green Zone mai tsananin tsaro a bagadaza.

Kakakin majalisar dokokin Kasar Mahmoud Al-Mashhadani yace fada ta gidan Talbijin cewa ‘yan jamalisar zasu zauna a gobe Jumma’a a tabakinsa domin su bijirewa ‘yan ta’adda.

Haka kuma Amirka da Britaniya sun la’anci harin kunar bakin wake da aka kai cikin majalisar dokokin kasar Iraq ayau Alhamis. Shugaba Bush na Amirka yace amirka tana tare da kasar Iraq kuma zata ci gaba da taimakawa demokradiyyar kasar domin ta sami damar tsayawa bisa sawayenta.

Sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleezza Rice ta ce wannan hari da aka kai ya nuna cewa ‘yan ta’adda sun dage ainun wajen ganin sun wargaza demokradiyyar kasar Iraq. Tace akwai munannan ranaku da kuma kyawawa bisa kokarin da akeyi na fatattakar ‘yan gwagwarmaya a Bagadaza, duk da haka kwamandodin suna kokari ne na ganin sun tabbatar da tsaron lafiya a kasar.

Sakatariyar harkokin wajen Birtaniya Margrett Beckett tafada a cikin wata sanarwa cewa wadanda suka kai wannan harin ba abinda suka tsinanawa ‘yan kasar illa kashe musu mutane da kuma barnar dukiyarsu.



XS
SM
MD
LG