Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Kolin ta yanke hukuncin cewa hukumar zabe bata da ’yancin hana wani tsayawa takara.


Kotun kolin ta yanke hukuncin cewa hukumar zabe bata da ’yancin hana wani tsayawa takara. Hukuncin da kotun kolin ta yanke a yau tayi watsi da hukuncin da wata kotu ta yanke kuma ta share fagge ga mataimakin shugaban Nigeria Atiku Abubakar yayi takara a zaben shugaban kasar da za’a yi a ranar asabar mai zuwa idan Allah ya kaimu.

Hukumar zaben Nigeria ce ta ce Atiku Abubakar bai cancanci tsayawa takara ba, bayan da wata hukuma ko kwamiti da shugaba Obasanjo ya kafa ta caje shi ko kuma ta same shi da laifin ci hanci da rashawa. Alhaji Atiku Abubakar wanda ya musunta wannan zargi ya kai karar hukumar zabe kotu.

A halin da ake ciki dai jam’iyar PDP wadda take jan ragamar mulkin Nigeria ita ke kan gaba a zaben gwamnoni dana wakilan Majalisun jihohi da aka yi shekaranjiya asabar. Sakamakon zabe da aka gabatar ya zuwa yanzu sun nuna cewa jam’iyar PDP ta samu nasara a akalla jihohi ashirin da daya daga cikin jihohi talatin da shidda. Jam’iyun masu hamaiya sunki amincewa sakamakon zapen akan cewa an yi magudi. Zaben na shekaranjiya asabar ta fuskancoi tarzoma harma an kashe akalla mutane ashirin da daya.

XS
SM
MD
LG