Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

wata yarinya ta mutu a Cambodia--mashassharar tsuntsaye


Wata yarinya ‘yar shekaru 13 da haifuwa a kasar Cambodia ta rasu asakamakon kamuwa da cutar mashassharan tsuntsaye, mutuwar da ta kawo adadin wadanda cutar da kashe a kasar zuwa mutum bakwai. Hukumar lafiya ta duniya da ma’aikatar lafiya ta kasar Cambodia sun tabbatar da wannan labari cewa yarinyar ta kamu ne da cutar nau’in H5N1 ta mashassharan tsun tsaye.

A kasar Indonesia kuma an sami wani Karin mutun da cutar ta kashe a kasar. jami’an kasar sunce wata yarinya ‘yar shekaru 15 da haifuwa itama ta rasu mutuwarta shi ya kara yawan wadanda suka mutu zuwa 73 a kasar. Hukumar lafiya ta Duniya bata tabbatar da wannan labarin ba kuma ya zuwa wannan lokaci dai tace mutane 63 ne a saninta suka mutu a Indonesia. Kasar Indonesia tafi kusan ko wace kasa yawan cutar mashasharan tsuntsaye.

Jami’an hukumar Lafiya ta duniya sunce mutane saba’in da daya ne suka kuma ya zuwa wannan lokaci daga bullar wannan cuta a shekara ta dubu 2 da 3.

XS
SM
MD
LG