Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan sanda a Jihar Kanon najeriya, sunce wani gunfun ‘yan bindiga ya kashe mutum goma sha uku


‘Yan sanda a Jihar Kanon najeriya, sunce wani gunfun ‘yan bindiga ya kashe mutum goma sha uku, lokacin da suka kai hari kan wani ofishin ‘yan sanda da sanyin safiyar yau Talata. ‘Yan sandan suka ce ‘Yan bindigar sun kashe shugaba, wato DPO na ofishin ‘yan sandan Panshekara, da matarsa da karin ‘yan sanda 11, a wannan hari da suka kai ido na ganin ido. Ana dai zargin ‘yan bindigar suna daga cikin wata kungiyar tsageru masu kishin addini.

Babu dai wata tabbacciyar hujja da zata danganta wannan hari da zaben da aka gudanar ranar Asabar din da ta gabata. Kafofin yada labarai na Najeriya sunce rigingimun siyasa sunyi sanadiyyar rasuwar a kalla mutum hamsin tun daga ranar wannan zabe. A halin da ake ciki kuma, hukumar zabe ta Najeriya tace zata bi umarnin hukuncin kotun koli ta najeriya, wadda tace a saka Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar a jerin masu takarar Shugaban Kasa da za a gudanar ranar Asabar mai zuwa. Mai magana da yawun hukumar, Philip Umeadi yace a halin yanzu ana daukar matakan cika wannan umarni. Hukumar dai tayi yunkurin hana Atiku Abubakar tsayawa, bisa zargin almundahana da dukiyar jama’a, zargin da mataimakin shugaban kasar ya musanta.

Masu sa ido na kasa da kasa suna tababar ko hukumar zaben zata iya gudanar da zaben mai zuwa, ganin yadda tashe tashen hankula da zarge zargen magudi suka addabi zaben da ya gabata. Kungiyar Kare Hakin Dan Adam ta Human Rights Watch, tace masu sa idanunta sunga magoya bayan Jam’iyyar PDP mai mulki, suna makare akwatunan zabe da kuri’u, a jihar Rivers da sauran wurare. ‘Yan sanda sun sanya dokar hana gudanar da tarukan siyasa a duk sassan kasar.

XS
SM
MD
LG