Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Jami’ar fasaha ta Jihar Virginia ta nan Amurka yace wani dalibin jami’ar, shine dan bindigar da ya kashe mutum 30, ya kuma kashe kansa a wani aji a jiya Litinin


Shugaban Jami’ar fasaha ta Jihar Virginia ta nan Amurka yace wani dalibin jami’ar, shine dan bindigar da ya kashe mutum 30, ya kuma kashe kansa a wani aji a jiya Litinin.

Saidai Mr. Chjarles Steger yace har yanzu ‘yan sanda basu gama bincuke ba. Bare su tabbatar ko shi kadai ne yayi harbe harben, har da wanda aka yi a dakin kwanan dalibai na jami’ar.

‘Yan sanda kuma basu bayar da wani bayani ba kan yiwuwar musabbabin harbe harben.

A yau an rufe Jami’ar, kuma da misalin karfe biyu na rana a yau talata, wato kimanin bakwai na yamma a agogon Najeriya, dalibai, da malamai da sauran ma’aikatan jami’ar zasu hadu da Shugaba Bush domin gudanar da addu’o’I ga mutum 33 da suka rasa rayukansu a wannan hari da aka ce shine mafi muni irinsa, a tarihin Amurka.

Wasu daga cikin daliban jami’ar da iyayensu, suna baiyana takaicinsu da yadda hukumomin jami’ar suka gaza bada umarnin rufe makarantar, tun da aka gudanar da harbe harben dakin kwanan dalibai, wanda da anyi hakan da ba a sami sukunin gudanar da na azuzuwan ba.

Steger ya shaidawa manema labarai a jiya Litinin cewa hukumomin jami’ar da ‘yan sanda sun dauka wanda ya gudanar da wadancan harbe harbe na dakin kwana ya ma riga ya fice daga jami’ar, amma daga baya sai gashi ya bulla a wani aji, inda ya kashe mutum talatin, ya kuma bindige kansa.

XS
SM
MD
LG