Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam’iyyun adawar Najeriya da ’yan kallon zabe masu zaman kan su sun ce zaben shugaban kasar bai yi ba, ya na cike da dimbin abubuwan da ba daidai ba.


Jam’iyyun adawar Najeriya da ’yan kallon zabe masu zaman kan su sun ce zaben shugaban kasar bai yi ba, ya na cike da dimbin abubuwan da ba daidai ba.

‘Yan takarar manyan jam’iyyun adawar kasar sun ce zaben na shekaranjiya asabar ya baci da bazuwar abubuwan rashin gaskiya. Daya daga cikin ’yan takarar, wato mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi kiran cewa a soke zaben da ya ce shi ne mafi munin da aka taba yi a kasar.

Kungiyar kasa da kasa ta karfafa demukradiyya da sanya idanu ta IRI mai cibiya a nan Amurka ta ce zaben bai cika ka’idojin kasa da kasa ba. Ta bada rahotannin yin aringizon kuri’u, da yin amfani da ’yan sanda a razana mutane, da kuma barin gungu-gungun mutane su kai ta yin zabe fiye da sau daya.

Shugabannin tarayyar Turai su ma sun bayyana damuwar cewa ba a bada dama ga ‘yan Najeriya sun yi zabe cikin ’yanci ba tare da fargaba ko tsoro ba. Wata kungiyar ’yan kallon zabe ta Najeriya mai suna(Transition Monitoring Group) ta yi kira cewa a sake yin zaɓen. Ta ce a wasu jahohin Najeriya 36 an bude rumfunan zaɓe a makare kwarai, a wasu jahohin ma sam ba a bude ba.

XS
SM
MD
LG