Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan bindiga sun kai hari kan wani Kamfanin mai na kasar China a gabashin Habasha, har kuma sun kashe a kalla mutum 74.


‘Yan bindiga sun kai hari kan wani Kamfanin mai na kasar China a gabashin Habasha, har kuma sun kashe a kalla mutum 74. Wata kungiyar ‘yan tawaye ta kwato ‘Yancin Yankin Ogaden tace ita ke da alhakin kai harin.

A wata sanarwa da ta bayar, kungiyar tace ta yiwa kamfanin rugu-rugu a yau Talata, ta kuma ce ba zata kyale a ci gaba da hakar ma’adinai a kasar ba muddin dai ba a baiwa al’ummar Ogaden ‘yancinsu na mulkin kai ba. Manajan Kamfanin mai na Zhongyuan, Xu Shuang yace an kashe ‘yan kasar China guda tara, da kuma ‘yan kasar Habasha guda 65, sa’annan kuma aka sace ‘yan kasar China guda bakwai. Ministan Yada labaran kasar Habasha, Herhane yace ‘yan bindigar sun kai harin ne a lokacin da ma’aikatan ke barchi. Ya zargi gwamnatin kasar Eritrea da marawa ‘yan bindigar baya, zargin da kamfanin Dillancin labaran Reuters yace Eritrea ta karyata.

XS
SM
MD
LG