Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An rantsarda Umaru Yar’adua shugaban kasar najeriya


An rantsarda Umaru Yar’adua shugaban kasar najeriya, bayan gagarumin nasara da ya samu a zabe da masu sa ido na kasa da kasa sukayi sukar cewa bashi da tasiri. Yar’adua yayi rantsuwar fara aiki yau talata a Abuja a wani Paretin Soja da akayi a fadar kasar, Abuja.

Dan shekaru 56 da haifuwa,kuma tsohon Gwamnan Jihar katsina,Yar’adua ya gaji Olusegun Obasanjo,wanda ya sauka,bayan yayi shekaru takwas yana mulki. Wannan biki shine karo na farko da Gwamnatin Farar hula zata mika mulki ga wata Gwamnatin farar fula a tarihin najeriya.

XS
SM
MD
LG