Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Albishir Ga Masu Sauraron Sashen Hausa Na Muryar Amurka


A ci gaba da kokarin kyautatawa masu sauraronsa, Sashen Hausa na Muryar Amurka zai kaddamar da Gasar Kacici-Kacici wadda ba a taba gani ko yin irinta ba a bana.

A lokacin da yake bayar da sanarwar kaddamar da wannan sabuwar gasa ta 2007, shugaban Sashen Hausa na Muryar Amurka, Sunday Dare, ya ce ba kamar yadda aka saba gani ana raba kyautar akwatin rediyo daya ko biyu ba, a wannan karon za a bayar da kyaututtukan akwatunan rediyo masu yawa, manya da kanana ga masu sauraro.

Shugaban na Sashen hausa ya ce abinda ya raba gasar ta bana da duk wata da aka saba gani, shine a bayan wadannan akwatunan rediyo, za a kuma bayar da kyaututtukan na'urorin sauti da sadarwa na zamani wanda ake kira "IPOD". Irin wannan na'ura ta IPOD zata bayar da mai ita damar sanya wakoki, ko hotuna, ko bidiyo, ko kuma dauko sautin labarai domin mutum ya ji a duk lokacin da yake bukata.

Sabuwar Gasar ta 2007 za a fara ta daga makon da zai fara ranar 24 ga watan Yuni. A kasance tare da Sashen hausa na Muryar Amurka domin jin cikakken bayanin wannan gasa a cikin shirye-shiryenmu.

Allah Ya bada mai rabo sa'a.!

XS
SM
MD
LG