Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawaye A Nijar Sun Yarda Jami'an Agaji Na Red Cross Su Yi Jinyar Sojojin Da Suka Kama


Ma’aikatan kungiyar agaji ta Red Cross sun ziyarci wani sansanin ’yan tawaye a arewacin Jamhuriyar Nijar domin jinyar sojojin gwamnati da aka kama.

Jami’an gwamnatin Nijar da na ’yan tawayen sun ce wannan tawaga ta kungiyar Red Cross zata bayar da agaji ga sojojin gwamnati wadanda suka ji rauni a makon jiya a lokacin da ’yan tawayen Abzinawa suka kai hari a kan wata cibiyar soja a garin Tezirzayt.

Wata kungiyar ’yan tawayen jamhuriyar Nijar dake kiran kanta Kungiyar Wanzar da Adalci a Nijar, ta dauki alhakin kai harin. ’Yan tawaye da kuma gwamnatin Nijar duk sun ce an kashe sojoji 15, aka kama guda 72 a zaman fursuna. Daga cikin wadannan sojoji da ake garkuwa da su, guda 43 sun ji rauni.

’Yan tawayen suka ce sun fusata ne da wani jawabin da shugaba Mamadou Tandja yayi kwanakin baya inda ya dora laifin tashin hankali kwanakin baya a arewacin kasar a kan ’yan daba.

XS
SM
MD
LG