Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yar'aduwa Ya Bayyanawa Duniya Irin Dukiyar Da Ya Mallaka


Sabon shugaban Nijeriya, Umaru Musa ’Yar’aduwa, ya bayyanawa duniya irin kadarorin da ya mallaka, matakin da ba a taba ganin irinsa ba a wannan kasar da zarmiya da cin hanci da rashawa suka zamo ruwan dare.

A yau jumma’a ’Yar’aduwa ya cika alkawarin da yayi lokacin yakin neman zabe, ya bayyana dukiyar da ya mallaka wadda ta kai ta dalar Amurka miliyan biyar. Har ila yau ya ce yana da gidaje da dama a arewacin Nijeriya inda iyalansa suke gudanar da harkokin kasuwanci mai yawa.

Wasu masu fashin baki sun ce bayyana dukiyar da ya mallaka da shugaban na Nijeriya yayi ya jaddada kudurinsa na yaki da zarmiya da rub da ciki kan dukiyar jama’a, kuma zai iya karfafa guiwar sauran jami’an gwamnati da su yi koyi da wannan.

Nijeriya ita ce kasar Afirka da ta fi samar da man fetur ga kasashen waje, amma kuma ana daukarta a zaman daya daga cikin kasashen da suka fi cin hanci da rashawa. Bankin duniya ya ce a cikin shekarun da suka shige an sace dubban miliyoyin dalolin jama’a a Nijeriya.

A bisa doka, tilas ne dukkan jami’an gwamnati su bayyana dukiyar da suka mallaka ga hukuma, amma kuma ba lallai ne su bayyana shi ga jama’a ba. Wannan shine karon farko da shugaba mai ci a Nijeriya ya bayyana dukiyar da ya mallaka ga duniya.

XS
SM
MD
LG