Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jama'a A Duk Fadin Nijeriya Suna Yin Tur Da Sace Yarinya Mai Shekaru Uku 'Yar Britaniya


Jama’a a duk fadin Nijeriya su na yin Allah wadarai da sace wata yarinya mai shekaru uku da haihuwa ’yar Britaniya da aka yi a yankin Niger Delta mai arzikin mai.

Uwar Margaret Hill ta ce masu yin garkuwa da ’yar tata sun tare motar dake dauke da wannan yarinya a kan hanyar zuwa makaranta jiya alhamis. Uwar ta ce wadannan ’yan fashin mutane sun bukaci da a biya su kudi kafin su sako ta.

Rahotannin farko sun ce mutanen sun yi barazanar kashe wannan yarinya idan har ubanta bai yarda ya mika kansa gare su a zaman fansarta ba.

Charles Dokubo, mai fashin baki a Cibiyar Nazarin harkokin Kasashen Duniya ta Nijeriya, ya bayyana satar yarinyar a zaman abinda ba zai karbu ba. Ya ce wannan ya nuna sauya alkibla baki daya daga gwagwarmayar siyasa ta neman karin kaso daga arzikin man fetur na yankin.

Ita ma babbar kungiyar ’yan tsageran Niger Delta ta MEND ta bayyana yin garkuwa da yarinyar mai shekaru uku a zaman abin kyama.

An sace ma’aikatan mai ’yan kasashen waje su kimanin 200 tun lokacin da aka fara yamutsi a yankin a shekarar 2006. Amma an yi imanin cewa wannan shine karon farko da aka sace wata yarinya ’yar kasar waje.

XS
SM
MD
LG