Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China ta hana  Shigo da Naman kaji daga Jamus da jahar Virginia ta Amirka zuwa kasarta.


kasar China ta hana shiga da kaji daga kasashen Jamus da janhuriyar Czech da kuma jahar Virginia anan Amirka saboda damuwarta game da cutar mashasharan tsuntsaye. Wannan mataki da China ta dauka ya biyo bayan matakai da wadansu kasashe suka dauka game da rahoton da aka samu a watan Yuni na bana na bullar kwayoyin cutar Nau’in H5N1.

Wata sanarwa da ma’aikatar Gona ta kasar China ta bayar ya nuna cewa kasar ta kuma hana kawo naman Alade daga Georgia, saboda rahoton bullar mashasharar wadansu irin tsuntsaye daga kasashen Afirka ayankun kasashen Turai. Sanarwar bata ce komai ba game da kasar Faransa wacce kwanan nan ta gano bullar cutar akasar ta.

A jahr Virginia, ana yanka Tolotolo guda dubu Hamsin da Hudu bayan da suka harbu da kwayoyin cutar, ko da yake basu kai abinda zai tsoratar ba. A makon jiya kuma China ta dakatar da shigo da naman Alade da kaji daga Amirka bayanda aka sami labarin bullar wadansu kwayoyin cuta da ake samu a magungunan da ake fesawa naman kaza da sauran nama domin a adana a kantuna.

XS
SM
MD
LG