Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Najeriya sunce an sake ‘yan kasar Rasha su shida da ake garkuwa dasu fiye da wata biyu


Hukumomin Najeriya sunce an sake ‘yan kasar Rasha su shida da ake garkuwa dasu fiye da wata biyu da suka wuce.An mika su ga Jami’an Gwamnati jiya Talata a yankin Niger delta mai arzikin mai dake kudan cin kasar.An sace ma’aikatan ne ranar uku ga watan shida,a harabar kamfanin kera karafan goran ruwa mai suna AlSCON mallkar wani kamfanin Rasha da ake kira Rusal.

A ribibin satar mutanen a gida da suke da zama ciki a garin Ikot Abasi ta kai ga hasarar ran matukin su,wadda ya sa Rasha ta bukaci hukumomin najeriya su daukimatakan gaugawa na ganin an saki mutanen.Satar mutane,akasari ‘yan kasashen ketare ya zama ruwa dare a kudancin Najeriya.

Kimanin Ma’ikata ‘yan kasashen ketare dari ne aka sace a yankin nan mai arzikin Mai,cikin wannan shekara. Akasarin wadanda ake garkuwa dasun,an sake su ba tareda ko kwarzana ba.

XS
SM
MD
LG