Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Musharraf A Pakistan Ta Janye Tuhumar Zarmiya Da Take Yi Ma Benazir Bhutto


Gwamnatin Pakistan ta yanke shawarar yin watsi da tuhumar zarmiya da take yi ma tsohuwar firayim minista Benazir Bhutto. Ministan zirga-zirgar jiragen kasa, Sheikh Rashid Ahmed, ya ce manyan jami’an Pakistan sun yarda da a yi watsi da wannan tsohuwar tuhuma da ake yi mata.

Malama Bhutto tana kokarin cimma yarjejeniyar raba ikon mulki da shugaba Pervez Musharraf, kuma wannan mataki na baya-bayan nan ya biya daya daga cikin muhimman bukatunta. Malama Bhutto, wadda tayi mulki sau biyu daga 1988 zuwa 1996, ta bar kasar Pakistan ta fara zaman gudun hijira bayan da aka tuhume ta da zarmiya da cin hanci.

Ta ce zata koma Pakistan ranar 18 ga watan Oktoba, shekaru takwas bayan da ta yi gudun hijira na son kanta domin tserewa gurfana gaban shari’a.

Wani kakakin jam’iyyar PPP ta Malama Bhutto, Farhatullah Babar, ya fadawa Muryar Amurka cewa babu abinda aka ce a game da bukatarta mafi muhimmanci, watau shugaba Musharraf ya ajiye mukamin kwamandan sojojin Pakistan kafin yayi takarar shugaban kasa ranar 6 ga watan Oktoba.

Shugaba Musharraf yayi alkawarin yin murabus daga mukamin kwamandan amma sai idan an zabe shi a wani sabon wa’adin shekaru biyar.

A saboda sa ran samun nasarar da yake yi, a yau talata aka zabi wani tsohon jami’in leken asirin kasar domin ya maye gurbin shugaba Musharraf a matsayin babban hafsan hafsoshin sojan kasar. Leftana janar Ashfaq Pervez Kiyani, zai karbi mukamin babban hafsan sojojin Pakistan idan shugaba Musharraf ya lashe zaben shugaban kasar.

XS
SM
MD
LG