Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Pakistan wani harin makami mai linzami ya lalata wata mabuyar yan yakin sa kai, ya kashe akalla mutane biyar


Rahotanin dake fitowa daga arewa maso yammacin Pakistan na cewa wani harin makami mai linzami ya lalata wata mabuyar yan yakin sa kai, ya kashe akalla mutane biyar. Jami’ai da mazauna yankin Waziristan sunce makami mai linzamin ya apkawa wani gida kusa da garin Miran Shah.

Mazauna yankin sunce wani jirgin saman yakin Amirka da sojoji karkashin jagorancin Amirka ke amfani dashi a kasar Afghanistan makwapciyar Pakistan ne ya kai harin. Ba’a ji ta bakin rundunar sojan Pakistan akan wannan al’amari ba.

A wani wuri dabam kuma, yan yakin sa kan Musulmi a yankin kwazazzabon Swat a arewa maso yammacin kasar sun jera mutane arba’in da takwas gaban ’yan jarida suka ce sojojin gwamnati ne da suka yi saranaa a lokacinda aka gwabza mumunar bata kashi.

Yan yakin sa kai dauke da makamai ne suka raka yan jarida zuwa garin Charabagh domin ganawa da wadanda aka kama. Su dai mutanen basu sanye da rigunan sarki kuma ba’a samu sukunin tabbatar da sunayensu ba. Jami’an Pakistan sun musunta cewa wasu sojoji sunyi saranda ko kuma an kama su.

XS
SM
MD
LG