Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kashe akalla farar hula guda daya a Mogadishu baban birnin kasar Somaliya


Shedun gani da ido sunce an kashe akalla farar hula guda daya a Mogadishu baban birnin kasar Somaliya a sabon fadan daya barke a yau juma’a wanda kuma ya hadasa rikicin jin kai. Ethiopia tare da goyon bayan sojojin gwamnati suka ne suka kai sumame wani wuri da suke zaton mabuyar ’yan yakin sa kan Musulmi ne.

Sojojin Ethiopia tare da taimakon sojojin Somaliya suna ta mumunar arangama da ’yan tawaye a birnin Mogadishu. Hukumar lura da ’yan gudun hijira ta Majaisar Dinkin Duniya tace fafatwar itace mafi muni da aka gani a birnin cikin ’yan watanin da suka shige, kuma tasa fiye da mutane dubu casa’in arcewa daga birnin tun ranar asabar. Faɗa mafi muni ya faru ne a ranakun asabar da lahadi kafin aka samu ɗan lafawar yan kwanaki.

Hukumar lura da yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya tace fiye da rabin mutanen da suka arce daga Mogadishu a wanan makon sun fake akan hanyar data doshi Afgooye, wani birnin dake kimamin kilomita talatin daga yammacin Mogadishu. Sabbin ’yan gudun hijirar sun iske wasu ’yan gudun hijira dubu dari waɗanda suma a farkon wannan shekara suka arce daga Mogadishu.

XS
SM
MD
LG