Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

PAKISTAN:Jakadar Amurka a kasar Pakistan Anne Patterson ta ja kunnen shugabannin Pakistan din da su hazarta tsaida ranar zabe


Jakadar Amurka a kasar Pakistan Anne Patterson ta ja kunnen shugabannin Pakistan din da su hazarta tsaida ranar zabe don kwantarda hankalin mutanen da suka razana da dokar ta-bacin da shugaban gwamnatin mulkin sojan Pakistan din, General Pervez Musharraf ya kargafawa kasar tashi.

A lokacin ganawarta da kusoshin hukumar zaben Pakistan din ne jakadar ta Amurka take matsa musu lamar su shirya gudanarda zaben nan da aeda, aka shirya za’a yi a tsakiyar watan Janairu na tafe, ba tareda chanja ranar ba.

Wannan ya biyo bayan rudamin da aka samu danganme da ko za’ayi wannan zaben a lokacin, ko ba za’a yi shi ba.

XS
SM
MD
LG