Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami’an Tsaron Najeriya Suna Tuhumar Wasu Mutane Da Alaka da Kungiyar al-Qaida


Hukumomin Najeriya sunce jami’an tsaro sun kama mutane da dama a jihohin kasar uku dake arewacin kasar bisa tuhumarsu da alaka da kungiyar al-Qaida. Kakakin Hukumar tsaro Ado Mu’azu ya gayawa manema labaru a ayau Litinin cewa Jam’ian sun kama mutane a jihohin Kano,Kaduna da Yobe.

Haka kuma yace jami’ai sun kwace kayan hada boma bomai da nakiyoyi ciki harda buhunan taki. Kakakin yace duk wadanda aka Kaman ‘yan Najeriya ne,sai dai bai fadi adadin wadanda aka kama ba.

Ahalin yanzu kuma gwamnatin Tarayyar Najeriyan ta kara kaso na kudade da zata kashe a yankin Niger delta mai fama da rigingimu a kasafin kudin badi,a kokarin da takeyi domin magance ‘gwagwarmaya daga yankin wadda ya nakasa hakar mai. Wakilin MA Gilbert da Costa yace gaggan kungiyoyin yankin basu gamsu ba

XS
SM
MD
LG