Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan sanda a Pakistan sun kame wani dan siyasar adawa, Imran Khan


‘Yan sanda a Pakistan sun kame wani dan siyasar adawa, Imran Khan, a daidai lokacin da yake fitowa daga maboyarsa domin ya shiga zanga zangar daliban dake nuna adawarsu ga dokar ta bacin da gwamnatin shugaba Musharraf ta ayyana.

‘Yan sandan sunce a basu umarnin su kame Khan, kuma sun mika masa takardar umarnin a lokacin da suka ci kacibus dashi, a Jami’ar Punjab, a tsagayarta ta Lahore, dake gabashin kasar a yat Laraba. Khan, wani shaharrren dan kwallon Cricket, wanda ke jagorancin wata karamar jam’iyyar adawa, ya shiga buya tun daga lokacin da Shugaba Musharraf ya kakabawa kasar dokar ta baci, mako biyu da suka gabata.

A halin da ake ciki kuma, tsohuwar Prime Minista Banazir Bhutto, wadda ke daurin talala a Lahore, tace dokar ta bacin da shugaba Musharraf ya ayyana shirme ce kawai, tunda bai fadi lokacin da zata kare aiki ba. Ga fassarar rahoton Wakilin Muryar Am,urka Barry Newhouse daga birnin Islamabad, kan halin da ake ciki a Pakista.

XS
SM
MD
LG