Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Pervez Musharraf na Pakistan ya kusa kammala shirye shiryen kaddamar da Gwamnatin Rikon Kwarya


Shugaba Pervez Musharraf na Pakistan ya kusa kammala shirye shiryen kaddamar da Gwamnatin Rikon Kwarya da zata maye gurbin Majalisar Kasar, wacce kuma zata gudanar da babban zaben kasar da ake shirin gudanarwa a watan janairu mai zuwa.

Janar Musharraf wanda wa’adin mulkinsa ke karewa a yau Alhamis, ya zabi shugaban Majalisar Dattawa Mohammedmian Soomro a matsayin Prime Ministan Rikon Kwarya. A gobe Juma’a za a rantsar da Soomro, wanda ake sa ran zai jagoranci zaben da Shugaba Musharraf yace za a gudanar ranar tara ga watan Janairu.

Shugabannin jam’iyyun adawa sunyi watsi da wannan alkawari, inda suka ce babu wani zaben kirki da za a iya gudanarwa a karkashin dokar ta baci. A halin da ake ciki kuma, manyan gidajen talbijin biyu wato Aaj da Dawn, sun dawo da watsa shirye shiryensu, bayan sun amince suyi aiki da sabuwar dokar da ta hana su yada duk wani bayani da ya soki lamirin gwamnati.

Tun da shugaba Musharraf ya aiyana dokar ta baci ranar uku ga wannan watan, aka rufe gidajen talbijin din guda biyu.

XS
SM
MD
LG