Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

OPEC tace kara yawan man da ake hakowa daga kasashen nasu ba zai yi wani tasiri a kan farashin man ba


Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man Fetur, OPEC tace kara yawan man da ake hakowa daga kasashen nasu ba zai yi wani tasiri a kan farashin man a kasuwannin duniya ba.

Ministocin, wadanda suka yim wani taro a yau, a birnin Riyadh na Saudi Arabia, sunce hauhawar farashin da ake fuskanta a halin yanzu, bashi da nasaba da karancinsa a kasuwannain duniya.

Taron Ministacin na yau shine zai share fagen taron shugabannin kasashen OPEC su 12, wadanda ake sa ran zasu baiyana matakin kungiyar na taimakawa wajen rage fitar iskar Carbon Dioxide, wadda ke haddasa dumamar yanayi. Wannan shine taro na uku da zai hada kan shugabannin kasashen, tun da aka kafa kungiyar a shekarar 1960.

XS
SM
MD
LG