Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma'aikatan Agaji A Bangladesh Su Na Ci Gaba Da Gwagwarmayar Kaiwa Ga Mutanen Da Suka Kubuta Da Rayukansu...


A yau litinin, ma'aikatan agaji a kasar Bangladesh su na ci gaba da gwagwarmayar kaiwa ga mutanen da suka kubuta da rayukansu daga mummunan hadarin ruwan sama dake tattare da mahaukaciyar guguwa a yankin kudancin kasar inda aka fi ganin barna.

Hukumomi suka ce wannan hadarin ruwan sama mai tare da mahaukaciyar guguwa da aka lakabawa suna Sidr, ya lalata hanyoyin mota, ya katse wutar lantarki da hanyoyin sadarwa ta waya, abinda ya nakkasa kokarin kungiyoyin agaji na ciki da wajen kasar.

Jiya lahadi, gwamnatin Bangladesh ta ce wannan gagarumin hadarin ruwan sama mai tafe da mahaukaciyar guguwa ya kashe mutane dubu biyu da dari uku a lokacin da ya abka kan kudancin kasar a makon da ya shige. Amma kungiyoyin agaji sun ce yawan wadanda suka mutu yana iya zarce haka nesa ba kusa ba. Kungiyar agaji ta Red Crescent ta kasar Bangladesh ta ce yawan wadaNda suka mutu yana iya kaiwa dubu goma a bayan an gano karin gawarwaki a yankunan dake cikin lungu wadanda har yanzu ba a kai gare su ba tukuna.

Bangladesh ta tura jiragen ruwan sojojinta tare da jiragen sama masu saukar ungulu na sojoji domin su dafa ma ayyukan agajin. Jiragen ruwan yaki na sojojin Amurka ma sun doshi kasar ta Bangladesh domin su taimaka wajen gudanar da ayyukan agajin.

Gwamnatin Amurka ta ce ta bayar da agajin farko na sama da dala miliyan biyu, kuma tana jigilar laidodi da kayayyakin tsarkake jiki da wasu kayayyakin masarufi domin wadanda suka kubuta da rayukansu. Shugaba Bush da mai dakinsa Laura sun mika ta'aziyyarsu ga mutanen kasar Bangladesh da abin ya shafa.

XS
SM
MD
LG