Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Akalla Shida Sun Mutu A Tashe-Tashen Hankulan Zaben Kananan Hukumomi A Jihar Kano


Hukumomi a Jihar Kano dake arewacin Nijeriya sun ce an kashe mutane shida, wasu daruruwan kuma su na tsare a sanadin tashe-tashen hankula masu alaka da zaben kananan hukumomi a Jihar.

Kwamishinan 'yan sanda a Jihar ta Kano, Aminu Yusufu, ya ce tashin hankali ya barke a sanadin gardama tsakanin magoya bayan jam'iyyu dabam-dabam kan sakamakon zaben da ba hukuma ce ta bayar ba.

Kakakin 'yan sandan jihar, ya fadawa Sashen Hausa na Muryar Amurka cewa an kama mutane fiye da dari biyu da hamsin, dauke da muggan makamai.

Rahotanni daga yankin sun ce an tabka magudin zabe, har ma wasu 'yan takarar sun fara daukar matakan ganin an soke sakamakon wannan zabe. Wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka ya ji ta bakin tsohon gwamna Rabi'u Musa Kwankwaso, wanda yayi tattaki zuwa hedkwatar 'yan sanda domin yin korafi a madadin jam'iyyarsu ta PDP, cewa tun ma kafin a fara kidaya kuri'un, har an ayyana sakamakon wasu mazabu.

Amma kuma gwamna Ibrahim Shekarau ya ce ya gamsu da yadda aka gudanar da wannan zaben, sai dai bai ji dadin tashe-tashen hankulan da suka biyo baya ba. ya ce hukumomi su na bincike domin hukumta dukkan wadanda suke da hannu a lamarin.

XS
SM
MD
LG