Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Talata Shugaba Pervez Musharraf Zai Isa Sa'udiyya...


Shugaba Pervez Musharraf na Pakistan zai isa Sa'udiyya yau talata domin tattaunawa da Sarki Abdullahi tare kuma da yin aikin Hajjin bana.

Wannan ziyara tana rura wutar rade-radin cewa watakila Janar Musharraf zai yi kokarin ganawa da tsohon firayim ministan Pakistan, Nawaz Sharif, wanda yake zaman gudun hijira a Sa'udiyya. Amma kuma Sharif, daya daga cikin manyan 'yan adawar Pakistan, ya ce ba zai gana da janar din ba, wanda ya hambarar da shi a wani juyin mulkin da babu zub da jini a 1999.

A wani labarin na siyasa kuma, alkalan kotun kolin da Janar Musharraf ya nada, sun kori akasarin kararrakin da aka shigar ana kalubalantar halalcin nasarar sake lashe zaben da janar din yayi. Atoni janar Malik Qayyum ya ce an yi watsi da kararrakin a saboda ba su cika sharrudan gabatarwa ba. Akwai sauran kara kwaya daya tak da za a saurare ta nan gaba cikin wannan makon.

'Yan adawa masu kalubalantar sake zaben Musharraf da aka yi cikin watan Oktoba sun ce ba su yarda da sabuwar kotun ba, wadda janar Musharraf ya sake mata fasali a bayan da ya kafa dokar-ta-baci a kasar.

XS
SM
MD
LG